1 John 2

1‘Ya’yana, na rubuta ma ku wadannan abubuwa domin kada kuyi zunubi. Amma idan wani yayi zunubi muna da matsakanci a wurin Uba, Yesu Almasihu, mai adalci. 2Shine fansar zunubanmu, ba ma namu kadai ba amma na duniya dukka. 3Ta haka muka san cewa mun san shi, idan mun kiyaye dokokinsa.

4Duk wanda yace, “Na san Allah” amma bai kiyaye dokokinsa ba, makaryaci ne gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5Amma duk wanda ya kiyaye maganarsa, hakika kaunar Allah ta kammala a cikin wannan mutum. Ta wurin haka muka sani muna cikinsa. 6Duk wanda yace yana cikin Allah dole ne shi da kansa yayi tafiya kamar yadda Yesu Almasihu yayi.

7Kaunatattu, ba sabuwar doka nike rubuta maku ba, amma tsohuwar doka ce wadda kuka ji tun farko. Tsohuwar dokar kuwa itace maganar da kuka ji tun farko. 8Amma yanzu ina rubuta maku sabuwar doka wadda gaskiya ce a cikin Almasihu da cikinku, saboda duhu yana wucewa, haske na gaskiya yana haskakawa.

9Duk wanda yace yana cikin haske amma yana kin dan’uwansa, yana cikin duhu har yanzu. 10kuma wanda yake kaunar dan’uwansa yana cikin haske babu dalilin tuntube a wurinsa. 11Amma duk wanda yake kin dan’uwansa yana cikin duhu, yana kuma tafiya cikin duhu, bai san ma inda ya nufa ba, domin duhu ya makantar da shi.

12Na rubuta maku, ya ku kaunatun ‘ya’yana, saboda an gafarta zunubanku domin sunansa. 13Na rubuta maku, ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku matasa saboda kun yi nasara da mugun. Na rubuta maku, yara kanana, saboda kun san Uban. 14Na rubuta maku, Ubanni, saboda kun san shi wanda yake tun daga farko. Na rubuta maku, matasa, saboda kuna da karfi, kuma maganar Allah tana zaune cikinku. Kuma kun yi nasara da mugun.

15Kada kuyi kaunar duniya ko abubuwan da suke cikin duniya. Idan wani yayi kaunar duniya, kaunar Uban bata cikinsa. 16Domin dukkan abubuwan da suke a cikin duniya, kwadayi na jiki, abin da idanu suke sha’wa, da rayuwar girman kai ta wofi, ba na Uban bane amma na duniya ne. 17Duniya tana wucewa tare da sha’awarta. Amma dukkan wanda ya aikata nufin Allah zaya kasance har abada.

18Yara kanana, sa’a ta karshe ce. Kamar dai yadda kuka ji magafcin Almasihu yana zuwa, ko yanzu ma magaftan Almasihu da yawa sun rigaya sun zo, ta haka muka san sa’a ta karshe ce. 19Sun fita daga cikinmu, dama su bana cikinmu bane. Gama idan da su namu ne da sun ci gaba tare damu. Amma da yake sun fita, ya nuna su ba na cikinmu bane.

20Amma ku kun karbi shafewa daga wurin Mai Tsarki, kuma dukkanku kun san gaskiya. 21Bana rubuta maku bane domin baku san gaskiya ba, amma saboda kun santa, kuma ba wata karya da ta fito daga gaskiya.

22Wanene makaryaci shine wanda yayi musu cewa Yesu ba Almasihu bane? Wannan mutumin shi ne magafcin Almasihu, tun da yayi musun Uba yayi musun Dan. 23Ba wanda yayi musun Dan kuma yake da Uban. Dukkan wanda ya amince da Dan yana da Uban ma.

24A game daku kuma, sai ku bari abinda kuka ji daga farko ya zauna a cikinku. Idan abin da kuka ji daga farko ya zauna a cikinku, kuma zaku kasance a cikin Dan da kuma Uban. 25Alkawarin da ya bamu kenan, rai na har abada. 26Na rubuta maku wadannan abubuwa ne game da wadanda zasu baudar daku.

27Game daku, shafewar daku ka samu daga wurinsa tana nan a cikinku, baku bukatar wani ya koyar daku. Amma kamar yadda shafewar da kuka karba a wurinsa ta koya maku dukkan abu, kuma gaskiya ne ba karya bane, tana nan a cikinku kamar yadda a ka koya maku, ku kasance a cikinsa. 28Yanzu fa, ‘ya’ya na kaunatattu, ku kasance a cikinsa domin sa’adda zai baiyyana mu zama da gabagadi ba tare da kunya ba a gabansa sa’adda zai zo. Idan kun sani shi mai adalci ne, kun sani dukkan wanda ke aikata adalci haifaffe ne daga wurinsa.

29

Copyright information for HauULB